6 Janairu 2022 - 15:54
Iran: Alkalin Alkalai Ya Ce Musulunci Na Da Tsarin Kare Hakkin Bil’adam Wanda Babu Shi A Duk Wani Addini

Alkalin alkalan kasar Iran Gholam–Hassan Mohsin –Ejiei ya bayyana cewa addinin musulunci yanada tsarin kare hakkin bil’adama wanda babu wani addini a duniya yake da shi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya bayyana haka ne a yau Laraba a lokacinda yake halattan taro na majalisar kare hakkin bil’adama na kasar Iran a ma’aikatar shari’ar kasar a nan birnin Tehran.

Mohseni-Ejeie ya kara da cewa kasar Iran ce zata nunawa duniya menene hakkin bil’adama, ba kasashen yamma wadanda suka shahara a ayyukan cin mutuncin bil’adama ne zasu nuna mana menen hare hakkin bil’adama ba.

Alkalin alkalan ya kammaka da cewa a halin yanzu kasashen yamma sun maida batun kare hakkin bil’adama a matsayin makami na yakar gwamnatin jumhuriyar Musulunci ta Iran a duniya, a dai lokacin babu wata kasa a duniya a yau face tana fuskantar wani nau’I na cin mutuncin bil’adama daga wadannan kasashe.

A yau kasashen yamma su ne a gaba wajen takurawa kasashen duniya da dama, da sunan kare hakkin bi’adama amma sojojin su da makirce-makircensu da danniya da kuma kissan mutanen ba basu san hawa ko sauka ba ya zama al-ada a garesu.

342/